
Yaya Dan Kwamba na shirin Gidan Badamasi ya aurar da Diyarsa ta uku
Yaya Dan Kwamba na shirin Gidan Badamasi ya aurar da Diyarsa ta uku
Ficaccan jarumin shirin Gidan Badamasi Nura Dan Dolo wanda aka fi sani da Yaya Dan Kwambo, ya aurar da Diyarsa ta uku.
Mun sami wannan cikekken rahoton ne daga shafin “Hausaloaded“, inda suka wallafa hotunan jarumin tare da Diyar tasa da kuma ‘yan uwa da abikan sana’ar tasa.
Ga cikekken rahoton da muka samu akan daura auren Diyar ta Nura Dan Dolo wato Yaya Dan Kwambo, wanda shafin na “Hausaloaded” suka wallafa.
Masha’Allah An Ɗaura Auren Diyar Yaya Dan Kwambo Allah Ya Bada Zaman Lafia.
An daura auren Diyar Fitaccen Me wasan Barkwancin nan a Masana’antar Kannywood Nura Dandolo wanda akafi sani da Yaya dan Kwambo acikin shiri me dogon Zango Gidan Badamasi.
An wallafa hotunan bikin a Shafukan sada Zumunta kuma sauran jaruman shirin na kwana Casa’in sun nuna masa kara inda sukaje har gida domin tayashi farin ciki.
Ga hotunan nasu a kasa domin ku kalla.