
Zama waje daya da saurayina a gidan mijina ya sanya shakuwar su tayi karfi har suna fita yawon shakatawa tare, cewar wata matar aure
Zama waje daya da saurayina a gidan mijina ya sanya shakuwar su tayi karfi har suna fita yawon shakatawa tare, cewar wata matar aure
Tamica Wilder wata mata ce dake zama a gida daya da saurayinta da kuma mijinta tare da yaranta, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.
Tamica ta hadu da mijinta tun shekaru sha daya da suka gabata, kuma ta sanar da shi cewa ba ta niyyar zama da shi shi daya.
Kamar yadda New York Post tanuna, tana son soyayya da maza da dama a lokaci guda, a lokacin data sanar da shi bai fahimta ba, amma yanzu ya gane.
Tamica ta bayyana yadda mijinta da saurayinta suka shaku da juna kwarai bayan barinsu suyi alaka da juna.
Bayan haihuwar yaranta biyu, bayan shekaru gona sha daya 11 da haduwarta da mijinta ta hadu da wani masoyin yayin wani biki da taje.
Bayan komawarta gida ta sanar da mijinta labarin sabon saurayin nata kuma tace bata son rabuwa da shi.
Bana da burin kin sake ganinsa, akwai wani abu da nake ji a jikina dangane da shi kuma soyayya ce wacce ba zan iya kyaleta ba, a cewarta.
Ta cigaba da haduwa da saurayin wanda daga bisani ta dawo da shi gidan mijinta inda tace, alakarsu ta kara karfi bayan cudanyar da yake yida yaranta, shakuwar su ta kai ga harsu na fita yawon shakatawa da mijinta tare da shi.
Rahoto daga👉 Labarun Hausa