
Labaran Hausa
Zargin madigo yasa Murja Ibrashim ta fashe da kuka tana karyatawa
Zargin madigo yasa Murja Ibrashim ta fashe da kuka tana karyatawa
Murja Ibrahim Kunya ‘Yar Tiktok ta fashe da kuka kan ana zarginta da cewa ita ‘yar madigo ce, matashiyar ta fashe da kukan ne a wata bidiyo inda ta karyata zaton da wasu ke yi a kanta na cewa ita ‘yar madigo ce.
Murja Ibrashim tace, ita dai a barta da tayi bidiyo ta dora shi akan sociyal midiya domin burge mutane da kuma nishadi.
Amma ashe cikin masu kallanta a soshiyal midiya da masu kallonta a gari a zahiri suna mata wannan mummunar kallon na madigo.
Sannan ta bayyana cewa, kila dai akwai wani laifi da ta aikatawa Ubangiji ne ya jarabceta da wannan zargin da ake mata, cikin hawaye take wannan bayanin nata.
Ga cikekkiyar bidiyon nan a kasa domin ku kalla.