
Zazzafan Martanin Rahama Sadau Kan Sayen Sunanta A Jerin Matan Da Zasuyiwa Tinubi Kamfen
Zazzafan Martanin Rahama Sadau Kan Sayen Sunanta A Jerin Matan Da Zasuyiwa Tinubi Kamfen
Jarumar finafinan Kannywood da Nollywood Rahama Sadau ta nesanta kanta da kasancewa cikin kwamitin mata na yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima a zaɓen shekarar 2023.
A ranar Asabar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ta bayyana sunayen mata ƴan kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar
Jerin sunayen ya ƙunshi wani ɓangare na masu nishaɗantarwa, wanda ke a ƙarƙashin jagorancin jarumar finafinan Nollywood Joke Silva. Jaridar The Cable ta rahoto.
An saka sunan Rahama Sadau a cikin kwamitin tare da sauran manyan jaruman Nollywood irin su Mercy Johnson, Toyin Adegbola, Esther Wright, Rose Odika, Hadiza Kabara, Fathia Balogun, da Sola Kosoko.
Saide Jarumar Tayi Martanin Da take magana a shafin Twitter akan bayyanar sunan ta a cikin kwamitin, Rahama Sadau ta ƙaryata kasancewa a cikin jirgin yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima.
Rahama Sadau tace ba a nemi shawarar ta ba kafin saka sunan ta a cikin jerin ƴan kwamitin.
Jarumar ta kuma yi mamakin yadda akayi har sunan ta ya shiga cikin ƴan kwamitin ba tare da iznin ta ba.
Wannan tsantsagoron ƙarya ce… Bani da masaniya akan wannan… Ban san ta yadda akayi suna na ya shigo cikin wannan jerin ba, bani da wata alaƙa kowace iri da wannan
Har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, jam’iyyar APC ba tace komai ba dangane da maganar da Rahama Sadau tayi.
Tinubu yana ɗaya daga cikin na sahun gaba a cikin ƴan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, tare da Atiku Abubakar na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Peter Obi na jam’iyyar Labour Party (LP)
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.