
Zazzafan wasan Mr 442 da Safara’u a Happy Independence a garin Maiduguri wanda ya dauki hankulan jama’a
Zazzafan wasan Mr 442 da Safara'u a Happy Independence a garin Maiduguri wanda ya dauki hankulan jama'a
Wadannan mawakan a yanzu haka suna chan kasar Maiduguri domin gudanar da wani wasa na murnar zagayowar ranar da aka bawa kasar Nigeria ‘yan cin kai, wanda ake gudanarwa a kowanne state a kasar nan domin nuna farin ciki.
Wannan Magana idan kuka kalleta haka take babu wadanda ake zagi a wannan garin kamar su fara’u da Mr 442, kuma abinda zai baku mamaki shine a duk lokacin da suka je waje sai aga ana shaukin zuwan su wanda ake yi musu wani abu domin nuna farin ciki wanda ba kowanne mawaki ake yiwa ba a wannan kasa ta Nigeria.
Mr442 shine wanda ya jagoranci tawagar sa zuwa wannan garin sabida suyi wasa kuma su nuna farin cikin su suma akan wannan rana, inda wannan wajen ya cika makil da mutane mata da maza duka a yayin wannan wasan wanda an yaba masa da nishadantar da mutane ta hanyar yin show.
Ga cikekkiyar bidiyon nan a kasa domin ku kalla.